Sarkin Katsina Ya Jaddada Kirarin Katsina @TaskarGizago #highlights
Taskar Gizago
0:00 / 0:00
Sarkin Katsina Ya Jaddada Kirarin Katsina @TaskarGizago #highlights
516 просмотров · 1 день назад
Taskar Gizago
2,94 тыс. подписчиков
516 просмотров · 1 день назад
Yadda Sarkin Katsina Ya Jaddada Kirarin Katsina
----------
Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Kabir Usman, ya jaddada kirarin Katsinawa, tare da kare martabar al'ummar Jihar Katsina da ma martabar Sarakunan Arewa gaba ɗaya.
Ga waɗanda suka san tarihi, ana yi wa Katsinawa da kirarin: KATSINA TA DIKKO ƊAKIN KARA, KUNYA GARE KU, BA DAI TSORO BA.
Sarkin na Katsina ya jaddada wannan kirari, inda ya fito fili ya faɗi wa masu mulki da 'yan siyasa gaskiya, a lokacin da wasu manyan malaman addini da manyan sarakuna suka kasa fitowa fili su fayyace wa masu mulki halin matsi da talauci da rashin tsaro da al'umma suke fama da su.
Sarkin Katsina ya ja hankalin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu, da suka kai masa ziyara a fadarsa da ke Katsina, inda ya bayyana masu cewa, kada su ɗauki alƙawuran da ba su iya cikawa.
Sarkin ya jaddada muhimmancin faɗin gaskiya ga al’umma, yana mai kira ga ’yan siyasa da su guji yi wa jama’a alƙawuran ƙarya ko na abubuwan da suka san ba za su iya aiwatarwa ba.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta kawo cikas ga harkokin noma a yankin Arewa maso Yamma, lamarin da ke shafar rayuwar manoma da tattalin arzikin yankin.
Yana mai kokawa da nuna damuwa kan yawaitar matsalolin tsaro, wanda hakan ke illata tattalin arziki da gurgunta sana'o'i da ayyukan yi, musamman noma da kiwo.
A ƙarshe Sarkin ya koka kan rufe masana’antu da kamfanoni a wasu sassan Arewacin Najeriya.
__________
@TaskarGizago #highlights #arewa #nigeria #africa #bashiryahuzamalumfashi #nigerianews #hausa #katsina