Перейти к содержимому

Mamman Shata waƙar Alhaji Audu Maijinka

Ibrahim Sheme

0:00 / 0:00

Mamman Shata waƙar Alhaji Audu Maijinka

859 просмотров · 2 нед. назад
Ibrahim Sheme
991 подписчик
859 просмотров · 2 нед. назад
TSOKACI KAN WAƘAR ALHAJI AUDU MAIJINKA TA ALHAJI MAMMAN SHATA KATSINA Daga Ibrahim Sheme A zamanin Jamhuriya ta Farko, Alhaji Audu Maijinka yana daga cikin manyan 'yan kwangila na gwamnatin Jihar Arewa. Hakan ya sa ya zama makusancin Firimiya, Sa Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato). Tun da fari, shi ɗan asalin Wushishi ne, a Jihar Neja ta yau. Sana'ar sa jinka, wato rufin ɗakin ƙasa da ake yi da haki, wato cuci. Da wannan sana'ar ya zo Kaduna, ya shahara, har ana yi masa laƙabi da ita. Da jarin sa ya yi ƙarfi sai ya shiga safarar rake, yana kwasar sa a mota yana kaiwa Guru (Nguru ta Jihar Yobe) da sauran garuruwan Arewa-maso-gabashin Nijeriya domin sayarwa a kasuwanni. Yana yi yana haɗawa da sana'ar sa ta jinka. Da Turawa suka kawo kwanon rufi, sai ya koma wannan ɓangaren, ya zama ɗan kwangilar rufi. An ce har kwangilar gine-gine ma ya yi wa gwamnatin Jihar Arewa. Harkar kwangila ta sa Alhaji Audu ya zama hamshaƙin attajiri. Lokacin da aka kashe Sardauna a 1966, da za a yi gwanjon motar da yake amfani da ita zuwa wurin aiki, Alhaji Audu Maijinka ne ya saye ta. A Janairu 2016, na yi hira da ɗan sa, wato Alhaji Usman Abdullahi Maijinka, a gidan su da ke Wushishi Road by Ahmadu Bello Way, Kaduna (lokacin ina bincike don rubuta littafin tarihin Shata da na yi mai suna 'Shata Ikon Allah!'). Ya faɗa mani cewa baban nasu ya rasu a cikin 1991, yana da sama da shekaru 90 a duniya. Ya ce ya bar matan sa da 'ya'ya biyu, mace da namiji. A cewar sa, Shata da Alhaji Audu Maijinka ba su shaƙu da juna ba har sai da Shatan ya yi masa wannan waƙa ɗaya tilo. Daga nan zumunci ya ƙullu a tsakanin su. Alhaji Mamman Shata Katsina ya nuna matuƙar hikima a waƙar, musamman inda yake kamanta mutum mai son yin shahara ta hanyar koɗawar maroƙa da kuma wanda ke da burin samun lada da za ta amfane shi a gobe ƙiyama. Ya ce in dai so kake a san ka, to ka rungumi su Shata, ka ba su kuɗi, su kuma su wasa ka, idan kuma lada kake nema, to ga almajirai can a bakin masallaci, ka je ka ba su sadaka. Waƙar, Mai taken "Ni Za Ni Kaduna Yawo Don In Ga Alhaji Audu Maijinka," tana daga cikin waƙoƙin Shata masu tsawo. Maroƙin da ake jin muryar sa a waƙar, fitaccen maroƙin nan ne da aka yi a Kaduna, wato marigayi Alhaji Mayau Yaro Gumel. Allah ya jiƙan magabatan mu, ya kyautata namu ƙarshen, amin.