Перейти к содержимому

ALHAJI MAMMALO SHATA, 'Yan Yara Duniya Labari Ce

Ibrahim Sheme

0:00 / 0:00

ALHAJI MAMMALO SHATA, 'Yan Yara Duniya Labari Ce

837 просмотров · 1 мес. назад
Ibrahim Sheme
991 подписчик
837 просмотров · 1 мес. назад
TSOKACI A KAN ZAMBON DA MAMMALO YA YI WA SHATA Daga Ibrahim Sheme A cikin 1977 ne dangantaka ta fara taɓarɓarewa tsakanin Alhaji Mamman Shata da mawaƙan Hausa na lokacin. Al'amurra da dama ne suka janyo hakan, har ta kai ga manyan mawaƙa da maroƙa sun kafa ƙungiya, suka ware Shata. Wasu yaran Shatan ma suka juya masa baya, suka rabu da shi. Ɗaya daga cikin su shi ne Alhaji Muhammadu Tasi'u, wanda aka fi sani da Mammalo Shata. Zaƙaƙurin mawaƙi ne, mai ɗimbin basira. Ya yi manyan waƙoƙi da dama. Ana ƙirga shi cikin yaran Shata duk da yake bai riƙa bin Shatan ba; shi makaɗi ne mai cin gashin kan sa, to amma idan Shata zai yi wasa shi ne zai share fage da waƙoƙin sa, daga nan sai ya shige cikin 'yan amshin Shata a yi aiki tare da shi. Da siyasar Jamhuriya ta Biyu ta shigo, sai ta yi tasiri cikin al'amarin saɓanin Shata da su Mammalo, har ta kai ga Shugaban Ƙasa Alhaji Shehu ya naɗa Mammalo muƙamin Sarkin Yaƙin Jam'iyyar NPN. A lokacin, shi Shata yana jam'iyyar GNPP ta Alhaji Waziri Ibrahim. Saɓanin Shata da Mammalo ya haifar da waƙoƙin zambo da Mammalo ya yi wa tsohon ubangidan nasa, ciki har da 'Gagarabadau' wadda ya ara a wurin Shatan, ya ragargaje shi, da kuma waƙar ''Yan Yara Duniya Labari Ce'. Ba kowa ne ya san cewa waƙar ''Yan Yara Duniya Labari Ce' zambo ne Mammalo ya yi wa Shata ba. An ɗauka nasiha ce kan rayuwa. Sai ma da ya fara da kiran mawaƙa da su daina zage-zage da zambo, amma kuma a cikin ta ya taɓo Shata da cewa a bakandamiyar sa: "Allah ya yarda, / Har yau ni ke yi, / Ku kau ba ku samo canji na ba, / Balle in zauna, / Wai har in ce zan huta." Mammalo ya ce masa a tasa waƙar: "Kun ce mana Allah ya yarda, / Mu ma gare mu Allahn ya yarda." Mammalo ya ci gaba da faɗin wasu baƙaƙen maganganun. Misali, ya ce masa: "In taƙamar ka tsafi kai tsafi, / Tsafi bai kai sarautar Allah ba." Kuma ya bugi ƙirji ya ce Shata da yaran sa ba za su fi shi zalaƙa ko basira ba. Haka kuma ya nuna cewa da ake cewa Shata mai kuɗi ne, yana da katafaren gida da motoci kaza-kaza, to shi ma ai ya yi gida a Kaduna (birnin Gwamna), "ga motar hawa na, ga babur". Kuma ya yi shaguɓe kan iƙirarin da ya riƙa yi cewa Shata ya satar masa waƙoƙi ya maida su nasa, ciki har da waƙar 'Ummaru Ɗan Ɗanduna Na Gwandu,' ya ce: "Ku daina satar waƙa ta." Haka kuma ya yi wa su Shata gugar zana, ya ce shi bai ci amanar kowa ba - da yake wasu sun riƙa cewa ya ci amanar Shata da ya rabu da shi ya bi Alhaji Bature Sarkin Magana wanda shi ne babban mai ja da Shata a lokacin. Da dai sauran su. Da ya kira kan sa "uban Hauwa," to ita ce babbar 'yar sa, kuma ita ce uwargidan shahararren makaɗin nan Alhaji Musa Ɗanbade yanzu haka. Mammalo ya ƙare waƙar da kamɓama babban ubangidan sa, wato Alhaji Umaru Nagoma Gwagwada, tare da jaddada cewa bai ci amanar kowa ba. A cikin 1983, Alhaji Mammalo Shata ya rasu a hanyar kai shi asibiti daga Faskari zuwa Funtuwa (Jihar Katsina yanzu). Sun je laccar yaƙin neman zaɓen Shagari a karo na biyu ne. Rasuwar sa babbar asara ce ga harkar kaɗe-kaɗen al'adun Hausa. Ya bar zuri'a mai yawa a Kaduna (inda gidan shi yake), wadda ta girma ta yi yaɗo sosai. Allah ya rahamshe shi, amin.